Yadda mace mai juna biyu za ta kula da kanta kafin haihuwa


 Yadda mace mai juna biyu za ta kula da kanta kafin haihuwa

Juna biyu lokaci ne mai albarka, amma kuma yana buƙatar kulawa ta musamman. Ga muhimman abubuwan da za su taimaka miki ki tsira lafiya, jariri ma ya tsira lafiya.


1. Ziyarar asibiti da wuri

Da zarar kin tabbatar kina da juna biyu, ki fara zuwa Antenatal. Wannan zai taimaka a gano jini, hawan jini, da girman jariri da wuri. Ki bi dukkan allurar da likita / ungozoma ta ba ki, musamman na tetanus da maganin ƙarar jini.


Idan kina da wata matsala da ta gabata, ko kina shan wani magani, ki faɗa wa likitanki tun da wuri, domin a duba ko ya dace.


2. Abinci mai gina jiki

Ki ci abinci daidai gwargwado:

• Tuwon dawa, shinkafa, doya, dankali don ƙarfi • Wake, ƙwai, nama, kifi don gina jiki • Ganye irin su alayyahu, zogale, da ƴaƴan itace irin su ayaba, lemu, gwanda • Madara da ruwa mai yawa, aƙalla kofi 8 a rana 

Ki rage gishiri mai yawa, sukari, abinci mai sosai, da abin sha mai gas.


3. Barci da hutu

Ki kwanta da wuri, ki samu barci na sa'o'i 7-8. Idan ciki ya yi girma, ki kwanta a gefen hagu, zai sauƙaƙa numfashi da jini ga jariri. Kar ki ɗauki kaya masu nauyi, ki rage tsayawa da dogon lokaci.


4. Motsa jiki mai sauƙi

Tafiya a hankali na minti 20-30, aƙalla sau 3 a mako, yana da kyau. Yana rage kumburin ƙafafu da ciwon baya. Ki daina duk wani motsa jiki mai tsanani sai da shawarar likita.


5. Tsafta da kwanciyar hankali

Ki wanke jiki kullum, ki sa tufafi masu sako da takalma marasa tudu. Ki nisanci damuwa. Addu'a, karatu mai sauƙi, da zama da mutanen da kike so, suna taimakawa.


Ki guji: shan taba, shan giya, maganin gargajiya ko na kantin magani ba tare da izinin likita ba.


6. Alamomin hatsari – ki je asibiti nan da nan idan kin ga: • Zubar jini • Ciwon kai mai tsanani da kumburin fuska / ƙafafu • Zazzabi mai ƙarfi • Jariri ya daina motsi • Ruwa ya fashe kafin lokaci • Ciwon mara mai yawan


7. maimaitawa  7. Shirya haihuwa

Daga wata ta 8, ki shirya jakar haihuwa: zane masu tsabta, kayan jariri, takardun asibiti, da kuɗin mota. Ki san inda za ki haihu, da wanda zai raka ki, da ko da dare ne


Allah yasa mudace

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Ma’aurata Za Su Ji Daɗin Zamantakewar Aure Ba Tare da Hadarin Zubar Ciki Ba

Dalilil da yasa wasu matan suke fara madigu

⚠️ “Wasu halaye marasa kyau a lokacin ibadan aure na iya haifar da matsaloli ga lafiyar mace…”