Dalilan Dawowar Fitsari Bayan Tsarki da Lokacin da Ya Kamata Ka Ga Likita
Assalamu Alaikum Likita. Ina da matsalar da ta daɗe tana damuna. Duk lokacin da na yi fitsari, bayan na kammala na yi tsarki, sai bayan na tashi sai wani ɗan fitsari ya sake fitowa kaɗan-kaɗan har yana ɓata min tufafi. Don Allah, mene ne zai iya jawo hakan, kuma me zan yi? Amsa Wa alaikumus salam. Matsalar da ka bayyana tana faruwa ga mutane da dama, musamman ma maza, kuma ba kai kaɗai ke fama da ita ba. A mafi yawan lokuta, wannan matsala tana faruwa ne saboda ragowar fitsari da ke kasancewa a cikin bututun fitsari bayan mutum ya gama fitsari. Da zarar mutum ya tashi, ya yi tafiya ko ya motsa jikinsa, sai ragowar fitsarin ya fito kaɗan-kaɗan. Sai dai kuma, ba koyaushe wannan ne yake haddasa matsalar ba. A wasu lokuta tana iya zama alamar wata matsalar lafiya da ke buƙatar binciken likita domin gano musabbabinta. Me Ka Iya Haddasa Wannan Matsalar? Akwai dalilai da dama da kan iya haddasa wannan matsala. Daga cikinsu akwai: Ragowar fitsari a cikin bututun fitsari bayan mutu...