💬 TAMBAYA: Aslm Dr, wani lokaci idan mukai sunnah da mijina sai wani ruwa yana dawowa min, me ke faruwa?
💬 TAMBAYA: Aslm Dr, wani lokaci idan mukai sunnah da mijina sai wani ruwa yana dawowa min, me ke faruwa?
🩺 AMSA:👇👇
Wa alaikum salam. Wannan abu ne da yake faruwa ga wasu mata, kuma a mafi yawan lokaci ba matsala ba ce.
👉 Dalilai na yau da kullum:
- Ragowar ruwa bayan mu’amala yana iya dawowa a hankali
- Jikin mace yana da tsarin tsaftace kansa bayan sunnah
- Idan kin tashi ko kin motsa nan da nan bayan an gama
👉 Wannan ba yana nufin rashin lafiya ba ne, kuma a yawancin lokaci ba ya hana daukar ciki.
❗ Amma ki kula:
Idan ruwan yana zuwa da:
- Wari mara kyau
- Kaikayi ko zafi
- Canjin launi (rawaya ko kore)
👉 To yana iya zama wata matsala ce ta infection, sai ki je asibiti domin a duba ki.
✅ Shawara:
✔ Ki kwanta na ɗan lokaci bayan sunnah
✔ Ki kula da tsaftar jikinki
✔ Ki guji amfani da magani ba tare da shawarar likita ba🚑
📢 Wannan abu ne na halitta—kar a firgita, amma a kula da alamomi!🚑


Comments
Post a Comment