Janyewar Sojojin Amurka daga Najeriya: Sojoji sun ce ba zai shafi yaki da ta'addanci ba


 Janyewar Sojojin Amurka daga Najeriya: Sojoji sun ce ba zai shafi yaki da ta'addanci ba

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da ficewar mafi yawan sojojin Amurka da aka turo kasar a farkon shekarar nan, don taimakawa wajen yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai.


Da yake magana da BBC a ranar Juma'a, kakakin rundunar sojin Najeriya, Michael Onoja, ya ce janyewar ba za ta sauya yadda suke gudanar da ayyukansu ba. 


Ya ce musayar bayanan sirri tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba, wani matsayi da ya yi daidai da na kwamandan rundunar sojin saman Amurka a Afirka, Janar Dagvin Anderson, wanda ya yi jawabi a wani taron manema labarai ranar Alhamis.


Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro da dama, daga hare-haren kungiyoyin masu ikirarin jihadi da ayyukan 'yan fashin daji, har zuwa rikice-rikicen da suka yadu daga arewa zuwa tsakiya da kudancin kasar.


Hadakar aikin tsaron Najeriya da Amurka ta kara karfi ne bayan Washington ta soki Abuja kan yadda take kare fararen hula masu rauni, inda ta yi ikirarin ana nuna wariya ga kiristoci a kasar. Najeriya ta karyata hakan, tana mai cewa rikicin yana da sarkakiya kuma yana shafar kowa da kowa.


Tun watan Disambar shekarar da ta gabata, dakarun kasashen biyu sun ce sun gudanar da hare-hare na hadin gwiwa kan maboyar 'yan bindiga, a matsayin bangare na kokarin da ake yi na dawo da zaman lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

Yadda Ma’aurata Za Su Ji Daɗin Zamantakewar Aure Ba Tare da Hadarin Zubar Ciki Ba

Dalilil da yasa wasu matan suke fara madigu

⚠️ “Wasu halaye marasa kyau a lokacin ibadan aure na iya haifar da matsaloli ga lafiyar mace…”